Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Ladabtar da Kasar Venezuela


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson

A wani mataki na matsa wa kasar Venezuela ta bi tafarkin dimokaradiyya ta wajen gudanar da zabe, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, ya ce Amurka na tunanin akalla takaita sayen mai daga kasar ko kuma uwa-uba ta kakaba ma ta takunkumi dungurungum.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce Amurka tana tunanin takaiata ko aza takunkumin sayen man fetur daga Venezuela a kokarin ta na matsawa kasar.
Ya bayyana hakan ne a zaman tattaunawar da sukayi da manyan kasar Argentina jiya lahadi a ziyarar da ya kai kasar, yace suna ganin yin hakan zai taimaka wajen tilastawa kasar ta gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci..
Amman Tillerson ya kara da cewa yana so a samo hanyoyin da zasu rage illar da takunkumin zata haifar ga kamfanonin man Amurka da wadansu kasashen da suka dogara samun mai daga kasar ta Venezuela.
Venezuela ita ce kasa ta uku mafi girma da take saida wa Amurka man fetur, kuma kamfanonin mai na Amurka sun ce hana shigo da man fetur daga kasar zai shafi ma'aika anan Amurka, kuma zai sa farashin mai ya karu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG