Wata tawagar Kiristoci daga Cocin Katolika, ta kai wa takwarorinta na addinin Islama ziyara a Birnin Konni da ke Jamhuriyar Nijar.
Ziyarar a cewar shugabannin na Katolika, mataki ne na kara karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin mabiya addinan biyu, tare da kara tabbatar da zaman lafiya.
“Zamanmu a nan Birnin Konni da Musulmi sai godiya, domin Allah ya ba mu sa’a,” na zaman lafiya. Daya daga cikin shugabannin Kiristocin ya fada wa wakilin Muryar Amurka Haruna Mamane Bako, a lokacin da ya tambaye shi dalilin wannn ziyara da suka kai wa Musulmi mabiya mazhabar Shi’a.
Malam Asman Bin Isa, daya daga cikin shugabannin kungiyar ta mabiya mazhabar Shi’a a Konni, ya ce wannan ziyara tana da matukar muhimmanci.
“Dama tun asali akwai alaka tsakanin Musulmi da Kiristoci, mun tattauna akan zaman lafiyarmu da yadda kowanne mu zai yi addininsa ba tare da ya shiga gonar wani ba.” Inji Malam Isa.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mamane Bako domin jin karin bayani:
Facebook Forum