Ministan harkokin cikin gidan a jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed, ya kare matakin baiwa sojojin Amurka dana Faransa sansanoni a cikin kasar.
Minista Bazoum wanda ya bayyana haka a hira da wakilin Sashen Hausa Sule Barma, yace galibin kasashe dake yankin Sahel, wadannan kasashe sun girke sojojin su a kasashen, amma ba zancen a ji 'yan kasar suna sukar wannan mataki.
Ministan na cikin gida, yace makasudin wannan mataki na samar da sansani kan sojojin ketare shine ganin yadda Nijar take kara fuskantar barzana da hare hare daga 'yan ta'adda daga kasashe da suke makwabtaka da ita.
Ya bada misali da yankin Agadez inda kasar take da dubban kilomita akan iyakarta, kuma bata da dakarun da zsu iya kare kan iyakar.
Da farko, Mallam Bazoum, yayi tsokaci kan dokar fadin albarkacin baki, wadda wasu suke fatali da ita, ta wajen amfani da kafofin sada zumunta suna nenan haddasa fitina cikin kasar.
Ga hirar da yayi da Sule Barma.
Facebook Forum