A bayanin da tayi gameda ranar iyaye a duk fadin dunya, Majalisar ta Dinkin Duniya cewa tayi; iyaye daga ko wani jinsi, addini, al'ada, ko kasa, sune masu renon yara, suna kimtsa su domin su tashi su zama mutane wadanda suke da kwanciyar rai, da zama mutane masu hazaka da aiki tukuru.
Majalisar tace iyaye sune harsashin gina ko wace al'uma.
A hira da Ibrahim Garba, wani matashi Yusuf El-Yakoub Rigasa, yace wannan rana tana da muhimmancin gaske saboda zata rika tunasarwa matasa da saura wadanda basa mutunta iyaye su gyara halinsu.
Kan rashin tarbiya tsakanin matasa kuwa, daya daga cikin dalilan da suka janyo haka inji Mallam Rigasa, shine wasu iyayen sun jingine nauyi da ya rataya akansu na yiwa 'yayansu tarbiya, saboda wasu dalilai na yau da kullum.
Daga nan ya shawarwaci matasa wadanda suke son su gama da duniya lafiya su mutunta iyaye.
Ga karin bayani.