Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutane Miliyan 265 a Duniya Zasu Fuskanci Matsalar Karancin Abinci - Hunger Project


Kimanin mutane miliyan 265 a duniya ake hasashen za su fuskanci matsalar karancin abinci a wannan shekara saboda annobar coronavirus, a cewar rahoton hukumar abinci ta duniya.

Alkaluman sun ninka fiye da mutane miliyan 130 da aka kiyasta za su yi fama da karanci abinci a shekarar da ta gabata.

Hasashen watan Afrilu ya zo ne ‘yan kwanaki kafin ranar 28 ga watan Mayu, ranar yaki da yunwa ta duniya, tsarin da wata kungiyar yaki da yunwa mai cibiya a birnin New York na Amurka ta yi.

Ana tsammanin annobar za ta kara zafafa mummunan hali da ake ciki, na 1 daga cikin mutum 9 ba su da ishashshen abinci, wanda ke nufin cewa mutane miliyan 820 suna fuskantar hadarin yunwa.

Kakakin kungiyar Hunger Project, Sara Wilson, ta ce mun sani wannan ya wuce harkar kiwon lafiya, ya zama rikicin yunwa da yake kara karuwa a kan mutane.

Yunwar da ake alakantawa da barkewar cutar COVID-19 da ake tsammanin matsin tattalin arziki zai haifar da tashin farashin kaya da kuma karanci abinci daga inda ake sarrafa shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG