Ministan Harkokin Cikin Gida Joseph Nkaissery ya ce saboda jerin hare-haren da su ka fuskanta daga tsattsaurar kungiyar nan ta al-Shabab da ke Somaliya, kasar ta Kenya ta kafa kwamitin aiki da cikawa da zai gudanar da aikin rufe sansanin.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya bayyana damuwa kan yiwuwar a tasa keyar 'yan gudun hijirar karfi da yaji.
Gwamnatin Kenya ta amsa cewa shawarar da ta dauka din za ta kuntata ma wasu 'yan gudun hijirar, sannan ta ce ya kamata kasashen duniya su dau matakan rage wahalhalun da 'yan gudun hijirar za su sha.
Kasar Kenya ta fara zana jadawalin rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab, mai dauke da Somaliyawa 'yan gudun hijira wajen 350,000.
WASHINGTON, DC —