Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kauyuka, Garuruwa 1,500 Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Jigawa - Hukumomi


Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan jihar Jigawa
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan jihar Jigawa

Ambaliyar ruwa da ake samu a wasu sassan Najeriya sanadiyyar matsanancin ruwan sama a kasar na ci gaba da mummunan tasiri ga rayuwa al’umr kasar, musamman mazauna karkara.

JIGAWA, NIGERIA - Yanzu haka dai shugabannin sarautun gargajiya a Jihar Jigawa daya daga cikin Jihohin Najeriyar dake fuskantar ambaliyar ruwa sun fara neman agaji ga talakawan su daga gwamnatoci da hukumomi masu zaman kansu, saboda mawuyacin halin da al’umarsu ke ciki.

Wata kididdiga da hukumomin Jihar ta Jigawa suka fitar ta nuna gonaki masu fadin hecta kimanin dubu dari biyu ne ambaliyar ruwa ta mamaye a kananan hukumomi 22, yayin da wannan iftila’in ya rusa gine-gine a kauyuka da garuruwa fiye da 1500.

Kananan hukumomin Ringim da Kafin Hausa da Auyo da Birnin Kudu da kuma Dutse na cikin yankunan da wannan ambaliya ta munana ainun.

Wasu daga cikin al’umar Jigawa da ambaliyar ruwa ta yiwa barna sun ce sun yi asarar kayan amfanin gona na miliyoyin naira, tare da rasa gidajen su. Tuni dai shugabanin gargajiya a Jihar suka fara neman a tallafawa wadannan talakawa nasu.

Ya roki gwamnatoci a dukkanin matakai da kuma hukumonin bada agaji su tallafawa al'umar sa, musamman ta fuskar kayan noman rani domin rage radadi ga mutane.

Hakimin gundumar Sindimina duka a yankin karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Adamu Mohammed Nakudu ya ce rayuwar talaka a yankin sa na cikin yanayi maras dadi, a don haka ya ja hankalin mahukunta da cibiyoyi masu zaman kan su da su tallafawa Jama'a.

Tuni dai masu kula da lamura ke hasashen cewa, al’umma a Jihohin Najeriya irin su Jigawa ka iya fuskantar kalubalen karancin abinci saboda wannan lamari, amma kwamishinan ayyuka na musamman a Jihar, Alhaji Auwalu Danladi Sankara ya ce gwamnati na daukar matakan samar da kayayyakin noma, musamman irin shuka mai yi da wuri, kamar dankali da kankana domin manoman Jihar su shuka bayan janyewar ruwa a wuraren da yayi ambaliya.

Wani al’amari da ambaliyar ruwa ta zo dashi Jigawa shine yawaitar hadduran kwale-kwale dake salwanta rayukan mutane, lamarin dake girgiza zukatan al’ummar jihar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Kauyuka, Garuruwa 1,500 Ambaliyar Ta Shafa A Jihar Jigawa - Hukumomi.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG