Ko da yake tun a makon jiya babbar kotun tarayya da ke Kano ta ba da umarnin haramci ga gwamnatin Kano, jami’ai ko hukumominta, cikin har da hukumar yaki da rashawa ta Kano daga gayyata ko yunkurin kama tsohon gwamnan ko iyalan sa ko kuma duk jami’in gwamnatin sa, amma wani ayarin kungiyoyin rajin yaki da rashawa na ci gaba da bayyana bukatar tsohon gwamnan ya mutunta sammacin hukumar yaki da rashawar ta Kano.
Comrade Kabiru Sa’idu Dakata shi ne ya jagoranci wani taron manema labarai game da wanna batu.
Dakata ya ce "kamar yadda muka tabbatar Jafar Jafar ya bayyana a gaban majalisar dokokin Kano ya ba da bahasi a shekarun baya dangane da wannan batu, haka zamu tabbatar da cewa shi ma Ganduje ya zo ya ba da nashi bahasin a gaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano cikin lumana, mu burin mu a tabbatar da adalci”
Ko dayake sun bayyana shakku game da gaskiyar wanzuwar wadannan kungiyoyi, bangaren tsohon gwamnan na Kano Abdullahi Umar Ganduje sun mayar da martani.
Barrister Abdul Adamu Fagge shi ne mashawarcin Jam’iyyar APC a jihar Kano ta fuskar harkokin shari’a da dokokin kasa.
Ya ce “ni ina ganin ba dai-dai ba ne, bai ma kamata suyi irin wannan kiran ba, irin wannan kiran idan ma za su yi, in dai sunan na su haka yake kamata yayi suyi akan tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, kasancewar akwai tuhuma a gaban hukumar EFCC akan sa dangane da rukunin gidaje guda uku, akwai tuhuma akan sa game da aikin hanyoyin kilo mita biyar a kananan hukumomi 44, akwai kuma white paper da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya rubuta akan sa, to da ya kamata su mayar da hankalin su akan wadannan batutuwa domin su ne tabbas”
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake daf da fitar da sunayen mutanen da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin ministoci kuma akwai bayanan da ke cewa, tsaffin gwamnonin Kanon 2 Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso kowannen su na muradun ganin sunan sa a jerin sunayen.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna