Shugaban mulkin sojin jamhuriyar Niger, janar Salihu Djibo ya yi fatali da bukatar da 'yan takarar shugabancin kasar takwas daga cikin goma suka gabatar ranar jumma'a, suna neman a dage zaben a kuma rusa hukumar zabe tare da girka wata sabuwar hukuma, wadda zata sake tsara sunayen masu zabe. Sun kuma bukaci a sake duba takardun 'yan takarar masu neman shiga majalisa da majalisar tsarin mulkin kasar tayi watsi da akasarin takardun 'yan takarar saboda abinda majalisar ta bayyana a matsayin rashin cancanta. A cikin jawabinsa a zaman taron da ya kira jiya da la'asar, wanda ya kunshi shugabannin rukunonin mulki da na addinai domin tattauna matsalar, shugaban mulkin sojan ya bayyana cewa ba zai keta dokokin da sabon kundin tsarin mulkin kasar ya tanada ba. Ya bayyana cewa za a gudanar da zagayen farko na zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa ranar talatin da daya ga wannan watan na Janairu kamar yadda aka tsara tun farko. Yan siyasar da suka halarci taron sun bayyana takaicin wannan matsayin suka kuma ce zasu shawarci magoya bayansu domin cimma matsaya kan ko zasu kauracewa zaben.
Gwamnatin sojan jamhuriyar Niger tayi watsi da bukatar da 'yan takarar shugaban kasar suka gabatar suna nema a dage zaben
Gwamnatin soji a Niger taki daga ranar zabe.