Rikicin Burkuna Faso ya samo asali ne saboda hambarar da gwamnatin wucin gadi da sojojin kasar suka yi makon jiya daidai lokacin da take shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.
Shawarar da masu daidaitawa suka bayar zata dawo da gwamnatin da sojojin suka kawar tare da yiwa sojojin ahuwa.
Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da aka shirya za'a gudanar 11 ga watan Oktoba na wannan shekarar za'a daga zuwa 22 ga watan Nuwambar wannan shekarar.
'Yan takaran da suke goyon bayan tsohon shugaban kasar da aka hambar bara Blaise Compaore da aka hanasu tsayawa zaben watan Oktoba yanzu suna da daman su tsaya.
Za'a gabatar da wannan shawarar wa taron koli na shugabannin kasashen Afirka ranar Talata su sa albarka.
Janar Gilbert Diendere wanda ya jagoranci juyin mulkin makon jiya ya fusata ne saboda an hana magoya bayan Campaore tsayawa zaben da aka so a yi watan gobe.
Dakarun dake tsaron fadar gwamnati sun yi garkuwa da shugaban kasar Maichael Kafando da firayim ministansa da wasu ministoci.
Kafin a farga wadanda suke adawa da juyin mulkin nan da nan suka fantsama kan tituna suna zanga zanga lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10 kana wasu fiye da 100 suka ji rauni.
Shi dai Campaore ya yi mulkin Burkina Faso har na tsawon shekaru 27 kafin a hambarar dashi bara biyo bayan zanga zangar kin jinisa da jama'ar kasar suka yi sanadiyar yunkurin da ya yi ya canza kundun tsarin mulkin kasar domin ya karawa kansa wa'adin mulki.