Yunkurin da Amurka ke yi na yakar ta’addanci a nahiyar Afirka na fuskantar matsaloli da dama, musamman ta fuskar yadda kungiyoyin ‘yan ta’addan ke sauya sheka kan kungiyoyin da suke yi wa mubaya’a tare da sauya manufofinsu.
A cewar jami’an tsaron kasashen yammacin duniya da takwarorinsu na Afirka, mambobin kungiyoyin ‘yan ta’adda na ci gaba da sauya manufofi da akidojinsu, lamarin da ke ci gaba da dishe layukan da ke sa a banbanta kungiyoyin da inda suka sa gaba.
Wannan a cewar jami’an, ya samo asali ne saboda yadda ‘yan ta’addan ke gogayya tare da nuna sha’awar yi wa kungiyoyi irinsu Al Qaeda da IS aiki.
A cewar Darektan da ke jagorantar runduna ta musmaman da ke yaki da kungiyar IS, Christopher Maier, ya zama dole sai an yi amfani da zurfin tunani wajen tantance kungiyoyin da suke yiwa mubaya’a, kafin a gane ainihin inda suka sa gaba.
Facebook Forum