Bayan kwanaki hudu da aka kwashe ana wata tattaunawa ta boye a Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia, wani jami’in gwamnatin Sudan ta Kudu ya ce bangarorin da ke fada da juna a Sudan ta Kudun, sun samu ci gaba kan batutuwan da suka shafi tsaro, amma ya ce gaskiya, ba a sami wani kwakkwaran ci gaba ba kan batun shugabanci da sauran manyan batutuwa da ke kawo tarnaki a rikicin kasar ta Sudan ta Kudu.
Ministan yada labaran kasar, Michael Makuei, ya ce bangarorin biyu, sun amince su hade dakarunsu wuri guda, amma kuma an samu cikas wajen amincewa da tsarin da za a bi wajen cimma hakan.
Ya kuma kara da cewa, har yanzu ba a cimma matsaya ba, kan yadda za a raba mukamai da sauran hukumomin gwamnati, wadanda suna daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a tsakanin gwamnatin ta Sudan ta Kudu da wakilan ‘yan adawa a wajen tattaunawar.
Su dai ‘yan adawan na zargin gwamnatin da kin sadaukar da wasu bukatunta, zargin da Minista Makuei ke musantawa.
Facebook Forum