Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Saliyo ta Kawo Karshen Dokar Hana Fita Domin Yakar Ebola


Titunan Saliyo wayas domin dokar hana fita
Titunan Saliyo wayas domin dokar hana fita

Kasar Saliyo ta anfana da taimakon dalamiliyan dari da saba'in da biyar da Amurka ta bayar domin yakar cutar ebola.

Kasar Saliyo ta kammala aiwatar da dokar hana fita ta kwana uku da ta ayyana da nufin shawo kan yaduwar cutar Ebola.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayyana jiya Lahadi cewa, ta sami nasarar kashe 75% inda ta ziyarci gidaje miliyan daya da dubu dari biyar.

Gwamnatin kasar Saliyo ta umarci mutane miliyan shida na kasar su zauna a gida ranar Jumma’a da asabar da kuma jiya Lahadi saboda tawagar likitoci su shiga gida gida suna tantance wadanda ke dauke da cutar Ebola su kuma wayar da kawunan jama’a kan yadda zasu kare kansu daga kamuwa daga cutar mai kisa.

Jami’ai sun ce za a ci gaba da zagawa cikin al’ummomin da aka lura suna cikin hadarin kamuwa da cutar a kasar.

Da alamu an gudanar da aiki lami-lafiya sai cikas da aka samu ranar asabar inda matasa suka kaiwa ma’aikatan jinya hari wadanda ke kokarin binne gawarwakin wadanda suka mutu da cutar Ebola a kusa da Freetown babban birnin kasar. Maharan sun arce bayanda aka kara turo ma’aikata domin kare masu aikin bison.

Kimanin mutane dubu biyar da dari uku suka kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo da Liberia da kuma Guinea bana, ta kuma kashe sama da mutane dubu biyu da dari shida.

Amurka ta bada gudummawar dala miliyan dari da saba’in da biyar domin shawo kan yaduwar cutar ta kuma tura dakaru dubu uku a yankin su gina asibitoci su kuma taimakawa yunkurin shawo kan cutar.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG