Gwamna Ibrahim Kashim Shettima yace shirin kafa hukumar da ake kira Northeast Development Commission shiri ne mai kyau kuma ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa.
Jihar zata yi iyakacin kokarinta ta tabbar da aiwatar da shirin. Shettima yace shiyar arewa maso gabashin Najeriya ita ce ta fi kowacce talauci a duk fadin kasar. Ita ce kuma koma baya kafin ma fitinar Boko Haram. Cikin shekaru shida da suka gabata babu ranar da ba'a kashe mutane a yankin tare da tashin bamabamai a wuraren ibada da ma kasuwanni. Lamuran da suka jawo hasara mai matukan yawan gaske.
Kafa hukumar ka iya zama hanyar tallafawa al'ummar shiyar yankin.
Barrister Muhammad Tahiru Monguno shi ne shugaban kwamitin. Yace zasu zaga duk jihohin dake shiyar arewa maso gabas musamman wadanda rigingimun Boko Haram ya daidaita. Hukumar da za'a kafa itace zata sake gina shiyar.
Onarebul Abdulrazak Namdas dan jihar Adamawa yace ko ba ma rikicin Boko Haram ba gwamnatocin da suka wuce can baya sun dade basu yiwa shiyar komi ba. Ko ayyukan gwamnatin tarayya babu su balantana na bankin duniya.
Ga karin bayani.