A Najeriya, hukuncin daurin shekaru 10 da wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke ma wani dan shekaru 13, wanda ta samu da laifin sabo, ya janyo takaddama da ra’ayoyi mabanbanta. Asusun Yara Na Duniya (UNICEF), na cikin masu adawa da wannan hukuncin, kamar yadda kafafen yada labarai, ciki har da CNN, su ka ruwaito.
An yanke hukunci ma Umar Faruk a kotun ta Shari’ar Musulunci da ke birnin Kano na arewa maso yammacin Najeriya, bayan da aka zarge shi da amfani da wani kalamin sabon Allah yayin wani musu da abokinsa.
An yanke masa hukuncin ne ranar 10 ga watan Agusta a kotun Shari’ar Musuluncin da kwanan nan ta yanke ma wani mai aiki a sutodiyon daukar waka mai suna Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa saboda laifin kalamun batunci ga Annabi Muhammad, a cewar lauyoyinsa.
Hukuncin da aka yanke wa Faruk ya saba ma Tanajin ‘Yancin Dan Adam da Walwalar Yara Na Kungiyar Tarayyar Afurka da kuma kundin tsarin mulki na Najeriya, a cewar lauyanshi Kola Alapinni, wanda ya gaya ma kafar labarai ta CNN cewa ya ma daukaka kara a madadin Faruk ranar 7 ga watan Satumba.
Jiya Laraba hukumar Asusun Yaran na UNICEF ta fitar da wata takardar bayani inda ta ke cewa ta yi matukar kaduwa da wannan hukuncin.
To saidai tsohon Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, shiyyar jahar Kano, Barrister Abdul Adamu Fagge, y ace akali ne kawai keda hurumin sake nazari ko sauya hukuncin da kotu ta zartar bisa dalilai kamar haka: tsallake wata sidirar doka daya kamata ayi la'akari da ita gabanin yanke hukunci.; rashin jin ta bakin wanda ake tuhuma kafin yanke hukunci; rashin gudanar da sahihin bincike; rashin hurumin sauraron shari'ar ga kotun data yanke hukuncin.
Shi kuwa Malam Mustafa Muhammad Dandume, daya daga cikin malaman addinin Musulunci a jahar Kano, ya ce addinin Musulinci ba ya take hakkin bil'adama. Alqur'ani da Hadisai da sauran littafan Shari'ar Musulunci sun yi tanadin karewa da mutunta ‘yancin bil'adama, musamman kananan yara. kuma da wadannan littatafai, ma’ana, da ayoyin Alqur'ani da Hadisai, Alkalan kotunan Musulinci ke aiki a fadin duniya wajen yanke hukunci akan duk wani Musulmi da aka tuhuma da aikata kowane irin laifi.
Don haka, ita ma kotun Shari'ar Musulunci ta Kano ta yi la'akari da wadannan kundaye da littafai ne wajen yanke hukunci akan Umar Farauk wanda kotu ta samu da laifin kalaman batanci ga mahalacci Allah ta'ala, kuma hukuncin ya yi daidai, muna goyon baya.
Hikimar irin wannan hukunci ita ce koya darasi ga sauran mutane domin a kyamaci aikata miyagun ayyuka ko kalamai.
Ga bayanin Barrister Abdul Adamu Fagge da wakilinmu a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari ya turo a sauti:
Sannan ga bayanin Shiekh Mustafa Muhammad Dandume da Mahmud ya turo a sauti:
Facebook Forum