Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: An Gudanar Da Taron Kungiyoyin Kasa Da Kasa Dake Gwagwarmayar Kare ‘Yancin Dan Adam


Taron Kungiyoyin Kasa Da Kasa Dake Gwagwarmayar Kare ‘Yancin Dan Adam
Taron Kungiyoyin Kasa Da Kasa Dake Gwagwarmayar Kare ‘Yancin Dan Adam

Kungiyoyin kasa da kasa dake gwagwarmayar kare ‘yancin dan Adam da wadanda ke ayyukan wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umar Nahiyar Afrika da na sassan duniya, sun gudanar da taro kan zaman lafiya da kuma martaba hakkin bil’adama a Kano.

Wakilan kungiyoyi masu zaman kan su dake aikace aikacen tabbatar da zaman lafiya da takwarorin su dake ayyukan kare hakin bani adama a matakin Najeriya da sassan Afrika ne suka halarci taro wadda ya wakana a nan Kano.

Kazalika, wakilai daga sassan duniya da kuma ofisoshin diplomasiyya na wasu kasashe sun bada gudunmawa ga zauren taron ta kafar sadarwa ta internet wato ZOOM

Rawar da hukumomi da kungiyoyi da cibiyoyin gwamnati da-ma daidaikun mutane ka iya takawa wajen wanzar da adalci da kare hakkin dan adam a kowane lokaci da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umomi sune batutuwan da suka mamaye ajandar taron.

Prof Buhari Isa shine babban Jami’in gudanarwa a ofishin kula da kungiyoyin diplomasiyya dana kare hakkin dan adam na Afrika, ya fayyace ayyukan da suka sanya a gaba domin cimma manufa. Ya ce suna ayyukan zamna lafiya da kare hakkin dan Adam da shirya zama na bita akan mahimmancin adalci da kuma kyautatawa.

A yayin taron wadda wakilai daga kasashen Turai da nahiyar Asiya suka bada gudunmawa ta kafar Zoom, kungiyoyin kare ‘yancin bil’adama dana diplomasiyya da zaman lafiya hadin gwiwa da School of LEADERSHIP ta Amurka sun karrama Hajiya Hassan Saminu Turaki da lambar ambassadon zaman lafiya bisa la’akari da kokarinta ta wannan fuska.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya ke cewa kunci da tsadar rayuwa a kasar na kara alkaluman cin zarafi da take hakkin bil’adama a tsakanin iyalai.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG