Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Sadarwa A Najeriya Suna Neman A Kara Kudin Yin Waya


MTN
MTN

Kamfanonin sadarwa a Najeriya suna neman a kara kudin yin waya da kashi 40 cikin 100 sakamakon tashin farashin gudanar da kasuwanci a kasar da su ka ce ana fuskanta.

Kamfanonin Sadarwar a karkashin Kungiyar Masu lasisin Sadarwa ta Najeriya ne suka aika da wannan shawara ga Hukumar Kula da Sadarwa ta kasa amma masu ruwa da tsaki na cewa Gwamnati ce ke da hurumin yin karin kudin waya ba Kungiyoyi ba

A takardar shawarar da Wadanan Kamfanonin sadarwa karkashin Kungiyar Masu Lasisin Sadarwa ta Najeriya suka aika wa Hukumar Sadarwa ta kasa wanda suka yi wa lakabi da Tsarin Tattalin Arziki da Tsaro a Bangaren Sadarwa, na son farashin layin waya ya tashi daga Naira 6.4 zuwa Naira 8.95 yayin da farashin sakon kar ta kwana wato sms ko text zai tashi daga Naira 4 zuwa Naira 5.61.

Kungiyoyin sun ce tabarbarewar tattalin arziki da cutar Korona ta kawo da kuma yakin Rasha da Kasar Yukurain ne suka haifar da hauhawar farashin makamshi da ya sa kudaden gudanar da aiyukan su ya hau da kashi 35 cikin 100.

Masanin harkar saarwa mai zaman kansa a Abuja Auwal Abdullahi yayi karin haske akan hujjojin da kungiyoyin suka bayar. Bisa ga cewarsa, suna da kwararan hujjojin kara kudin wayar kasancewa farashin komi ya tasha sakamakon mastsaloli da aka fuskanta da suka hada da barkewar annobar korona da ya haifar da tsadar kudin canji. Akwai kuma batun haraji da aka karawa kamfanonin wayoyin salulan, sai kuma tsadar man dizel. Yace wadannan duka na daga cikin hujjojin kamfanonin na neman kara kudin waya.

A hirar su da Muryar Amurka, wadansu masu amfani da wayar sadarwa sun bayyana takaicin su kan wannan shawarar, tare da yin kira ga hukumomi su yi watsi da wannan shirin da suka ce zai kara nawaitawa talakawa.

A nashi bayanin, masanin kundin tsarin mulki da shari'a Barista Mainasara Umar ya ce kungiyoyi basu da hurumin karin kudin waya

Shi ma shugaban hulda da manema labarai na Hukumar kula da Sadarwa Ike Adinde ya bayyana cewa Hukumar Sadarwa ta kasa ce kadai ke da hurumin kara kudin waya a Kasar.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda cikin sauti:

Kamfanonin Sadarwa A Najeriya Suna Neman A Kara Kudin Yin Waya-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG