Kamfanonin Amurka da ke kasar China sun ce suna samin cigaba, to amman sun damu da yadda aka kafa dokokin da su ka ce na nuna fifiko ga kamfanonin ‘yan kasar.
A wani binciken da Cibiyar Habbaka Kasuwancin Amurka ta yi a China, kashi 85% na wadanda su ka yi bayani sun ce sun sami riba a harkokinsu na China a 2010, a sa’ilinda 83% su ka ce wannan shekarar za su kara yawan jarin da su ke sakawa a wannan kasa wadda ita ce ta biyu a arziki a duniya.
To amman kusan kashi uku bisa hudun wadanda aka tambaya sun ce ana nuna wariya ga kamfanonin kasar waje a tsarin bayar da lasisi, kuma kashi 40% sun ce kamfanoninsu za su cutu da manufofin kasar na taimaka wa kamfanonin kayan kere-keren kasar su sami kwangilolin gwamnati.
Firaministan China Wen Jiabao ya gaya wa wani ayarin shugabannin kamfanonin kasashen waje a wani taro jiya Litini cewa yakamata a yi wa kamfanonin kasashen waje irin yadda ake yi wa kamfanonin kasar, kuma kamata ya yi a kare masu ‘yancin mai kirkira.
Mr. Wen ya ce yakamata kamfanonin kasashen wajen da ke saka hannun jari a China su yi la’akari da wasu abubuwa, ciki har da tsayayyen tsarin siyasar kasar da kuma dokokin da ke samar da kariya, matukar su na fatan yin nasara.