Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban Haiti, Aristide yana kan hanyarsa ta komawa gida


Former Haitian President Jean-Bertrand Aristide (file photo)
Former Haitian President Jean-Bertrand Aristide (file photo)

Tsohon shugaban kasar Haiti, Jean-Bertrand Aristide, ya kawo karshen zaman gudun hijirar shekaru 7, ya kuma doshi kasarsa duk da gargadin da Amurka ta yi masa na yin hakan. Jiya alhamis jirgin saman Mr. Aristide ya tashi daga filin jirgin saman Johannesburg a Afrika ta kudu inda ya bayyana wannan a zaman wata rana mai tarihi. Yau jumma’a ake sa ran zai sauka a kasarsa ta Haiti.

Tsohon shugaban kasar Haiti, Jean-Bertrand Aristide, ya kawo karshen zaman gudun hijirar shekaru 7, ya kuma doshi kasarsa duk da gargadin da Amurka ta yi masa na yin hakan. Jiya alhamis jirgin saman Mr. Aristide ya tashi daga filin jirgin saman Johannesburg a Afrika ta kudu inda ya bayyana wannan a zaman wata rana mai tarihi. Yau jumma’a ake sa ran zai sauka a kasarsa ta Haiti. A filin jirgin saman, Mr. Aristide yace shi da maidakinsa sun yi farin ciki matuka ganin cewa zasu koma Haiti, kuma su ma al’ummar haiti su na murna sosai kan cewa zai koma kasar. ‘Yan tawaye dauke da makamai sun kori Mr. Aristide daga kan mulki a watan Fabrairun 2004, kuma tun lokacin yake zaune a kasar ATK. Tun fari a jiya alhamis, minista mai kula da ayyukan fadar shugaban kasa na Afrika ta kudu, Collins Chabane, yace jami’an kasar Haiti sun ba tsohon shugaban Fasfo, saboda haka Afrika ta kudu ba zata iya rike shi ta hana shi tafiya kasarsaba. Kakakin majalisar tsaron kasa ta nan Amurka, Tommy Vietor yace Amurka ta damu sosai da komawar Mr. Aristide Haiti, yana mai gargadin cewa tana iya gurgunta zaben shugaban kasar da ake shirin sake gudanarwa ranar lahadi. Har ila yau Vietor yace shugaba Barack Obama ya kira shugaba Jacob Zuma na Afrika ta kudu a wannan makon inda ya bayyana masa wannan damuwa. Mr. Aristide ya bayyana kwadayin komawa Haiti a bayan da shugaban kasar dan kama karya Jean-Claude Duvalier, ya koma haka kwatsam ba zato ba tsammani a watan Janairu.

XS
SM
MD
LG