Kamfanin na NNPC dai ya canja shawara ne sakamakon yadda ‘yan kasa suka yi ta yi korafi game da yadda suka yi ta fuskantar rashin samun mai da bin dogayen layi a gidajen mai musamman a birnin tarayya Abuja.
Shugaban kamfanin man na NNPC, Alhaji Mele Kyari ne ya bayyana haka a hira da Muryar Amurka.
Ya ce tunda sun dauki wannan mataki na rashin kara farashin man ba amfani mutane su shiga fargaba su tashi suna rugawa gudajen mai don saya da tarawa.
Ya kara da cewa duk Depot din su na gwamnati da kuma inda aka saba sayar wa akwai wadataccen mai, kuma za a iya zuwa a duba don tabbatar da haka, shi ya sa babu amfanin yin rubibi akai.
Shugaban ya ce duk da cewa tallafin da ake samu daga gwamnati babu shi yanzu amma suna la’akari da wahalar da jama’a su ke ciki kuma kowanne irin farashi za a sa, za a duba halin da jama’a ke ciki.
Saurari hirar Alhaji Mele Kyari da Halima Abdul’Rauf cikin sauti:
Karin bayani akan: Alhaji Mele Kyari, NNPC, Nigeria, da Najeriya.