Yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka, Kyari ya ce Najeriya ta hada kai da kasar Rasha a kokarin da take yi na ganin ta gudanar da gyaran wadannan matatun man.
"Najeriya tana bukatar mai da yawa, don wadatar da 'yan kasa, don haka ko da an kammala gyaran wadannan matatun ba za su wadatar da kasar ba, Abin da Najeriya ke bukata ya haura ganga miliyan hamsin."
A dalilin haka ya ce akwai bukatar masu hannu da shuni a kasar su tashi tsaye wajen saka jari don kafa matatun mai masu zaman kansu, kamar yadda Dangote ya fara, idan aka samun yawaitar wadannan za'a iya samun saukin karancin mai a Najeriya.
Matatun man na Kaduna da Warri sun Jima ba sa aiki.
Shugaban kamfanin na NNPC ya kuma shaidawa Muryar Amurka cewar, "a shekarun baya an tafka kura-kurai, yanzu suna aikin gyaran kura-kuran, irin yadda ba'a nazarci yadda matatun man ke aiki ba da kuma irin adadin da za su iya samarwa."
Sai ya kara da cewar "ba za'a ce abin kunya ba ne ga kasa irin Najeriya mai arzikin mai ta koma tana shigo da mai daga kasashen ketare ba. Amma abin da ya sani shi ne, idan ka yi kuskure to babu laifi idan ka dauki laifinka don neman hanyar gyara, wanda yanzu haka shi suka sa a gaba."
Ga cikakkiyar hirar da suka yi da Yusuf Aliyu Harande.
Facebook Forum