Batun taso keyar 'yan Najeriyan zuwa gida na tada hankalin mahukunta a kasar saboda tanadin da ya kamata su yi kafin mutanen su iso.
Amma tuni majalisar wakilan tarayya ta kafa kwamitin aiki da cikawa da ya kunshi wakilai daga shiyar arewa maso gabashin Najeriya dake cikin majalisar. Su ne zasu je kasar Kamaru domin tattaunawa da mahukuntar kasar ta Kamaru.
Onarebul Lawal Garba yana cikin kwamitin kula da 'yan gudun hijiran na majalisar wakilan ya kuma bayyana matakan da zasu dauka domin dawo da 'yan Najeriyan.
Yace sun tattauna batun a majalisa. An kafa kwamitin mutanen da zasu je Kamaru tare da duk 'yan majalisar wakilan da suka fito daga yankin arewa maso gabas.
Akwai wani kwamiti kuma da zai tafi Bakasi. Zasu kuma sadu da gwamnan Adamawa saboda ta jiharsa ce za'a kawo 'yan gudun hijiran.
Su ma 'yan majalisar dattawa lamarin ya tayar masu da hankali kamar yadda Sanata Abdulaziz Murtala Nyako ya bayyana. Yace kamar Kamaru ta yi dan gaggawa. Kamata ya yi ta karawa Najeriya dan lokaci amma zasu ga yadda zasu taimaka.
Ga karin bayani.