Mai fashin bakin al’amuran yau da kullum kuma Malamin Jami’a Dakta Khalifa Dikwa, yace tun farkon fitowar kungiyar Boko Haram ya janyo hankalin gwamnatin da ta gabata, kan cewa akwai abin dubawa kan mutanen, domin dukkan mayakan ta’addancin duniya abu guda ne.
Sunayen kungiyoyin ta’addancin ne kawai suka bambanta. Halinsu daya da sauran ‘yan bindigar da ke kasar Samaliya da Afghanistan da Pakistan da Arewacin Kenya da sauran kasashen Larabawa.
Wanda gwamnati a wancan lokacin ba ta saurari maganar ba, inda yanzu haka mutanen kasa ke ganin gaskiyar abinda Dakta Dikwa ke fada. A cewar Dakta, tun da aka sami sauyin mulki a Najeriya aka samu ci gaba ta bangaren soja da masu aikin bada bayanan sirri.
Idan aka duba a baya, za a ga tamkar ba sa son yakar masifar a wancan lokacin, har ta kai aka raunana harkar tsaro a kasar da sanin gwamnatin Tarayya ta lokacin da ya shude din. Yanzu haka dai da alamu an ci galaba, domin baki daya an shafe kungiyar Boko Haram.
Inda babu wani waje da suke taruwa kamar yadda suke yi a baya, na yin gungu tare da yin tafiyar fiye da kilomita 100 ko 150 su je garuruwa suna barna da kashe-kashen mutane. Haka kuma idan suna bukata, ba a rufe musu kofar da za su dawo su tuba ba domin a zauna a sulhunta ba.
Saurari Hirar Usman Kabara da Dr. Khalifa Dikwa.