Yaki da cin hanci da rashawa da ma sauran ayyukan almundahana ka iya shafar kowa amma ba lallai ne wadanda abun ya shafa su fada hannun jami'an yakin a lokaci guda ba.
A wasu lokutan ma akan samu jami'an yakin su ma da zarmewa yayinda da hukumar dake yaki da wannan bala'in ke cewa ta kan hukumtasu bisa tanadin doka.
Saidai babu mamaki yakin ya fi shafar jami'an gwamnatin da ta gabata domin kau da kai kan wasu laifuka kamar yadda wani tsohon jami'in banki Alhaji Garba Umar Yobe ya fada.
Yana mai cewa bayan wata gwamnati ta bar sauka sau tari jami'anta ne za'a bincika kodayake watakil yawancin abubuwan an yisu ne ta fuskar gwamnati. Yace abun da wannan gwamnati ta bullo dashi na bada tukwuici ga wanda suke tsegunta mata inda aka boye dukiyar jama'a yayi daidai. Ya ba da gaskiya cewa a karshe cin hanci da rashawa zasu kasance basu da anfani. Duk wanda yayi ya bata wa kansa lokaci da sunansa ne.
Ganin yadda masu rike da mukaman gwamnati suke walwala yayinda talakawa ke tagumi ya kara karfafa zargin samun mukami a Najeriya tamkar hanyar tara arziki ne da abun duniya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum