Ana ci gaba da sa’insa kan belin da mai shara’a Nathan Musa, alkalin alkalan Adamawa ya baiwa tsohon gwamnan jihar Barrister Bala James Ngillari wanda ya yi zaman katso na kwanaki ashirin da daya daga wa’adin shekaru biyarda shi alkalin alkalan ya yanke masa.
Mai Magana a madadin lauyoyan dake kare tsohon gwamnan Sam Ologunorisa, Barrister Obed Wadzani ya fadawa taron manema labarai a cibiyar ‘yan jaridu ta Yola cewa kaifin hujjojin da suka gabatar gaban kotu sune kotun ta duba ta bada belinsa ba takardar da hukumar gidan yarin Yola ta rubuta ta gabatar gaban shara’a ba.
A daya bangaren kuma, kwamishanan shara’a na jihar Adamawa Barrister Silas Sanga ya ce suna kalubalanta sahihancin takardar saboda suna da takardar da kwana daya bayan kotu ta bada belinsa shugabancin gidan kason ya shaida a rubuce cewa tsohon gwamnan yana cikin koshin lafiya.
A jam’iyyance inji shugaban PDP na jihar Adamawa Barrister Abdulrahaman Bobboi da alamun ana ma ‘ya’yanta bita-da-kulli saboda kawo yanzu ‘ya’yan jam’iyyar uku na zaman katso.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Facebook Forum