Babban sufetan ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya bayyana cewa akwai lauje cikin rahoton kungiyar kare hakkin bil’adama na Amnesty International, da ya yi nuni da cewa, jami’an rundunar sun yi amfani da karfi fiye da kima a kan masu zanga-zangar neman a kawo karshen sashen rundunar 'yan sanda SARS.
Rundunar 'yan sandan ta Najeriya ta bayyana matsayarta kan rahoton ne cikin sanarwar da kakakinta Frank Mba ya fitar a yau Juma’ah.
Babban sufetan ya kuma jaddada cewa, jami’an sa sun yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata, kuma wasu daga cikin su sun sadaukar da kansu domin tabbatar da dorewra zaman lafiya a yayin da aka fuskanci rikice-rikice a wasu sassan kasar a lokacin zanga-zangar.
A cewarsa, jami’ai 22 sun rasa rayukansu a yayin da aka lalata caji ofis da wasu sashen rundunar ‘yan sanda 205 a duk fadin kasar.
Muhammad, ya kuma bayyana cewa, a cikin rahotonta, kungiyar Amnesty International, ta daura laifi a kan 'yan sanda sakamakon zargin cin zarafin wasu masu fafutukar neman sauyi a aikin ‘yan sanda, inda aka yi nuni da cewa an yi amfani da karfin da ya wuce kima.
Kungiyar Amnesty International dai ta ce masu zanga-zanga fiye da 12 sun rasa ransu a lokacin da zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma, sai dai babban sufetan ‘yan sanda, ya ce akwai yaudara cikin rahoton kuma ba bu kamshin gaskiya a cikin lamarin, yana mai cewa sakamakon dukka shaidun da aka tattara ya yi nuni da cewa akwai akasi.
Facebook Forum