Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ka'idoji Bakwai Na Kungiyar Bada Agajin Gaggawa


'yan Kungiyar Bada Agajin Gaggawa
'yan Kungiyar Bada Agajin Gaggawa

Kungiyar bada agajin gaggawa wadda akafi sani da Red Cross na taka rawar gani wajan ba jama'a taimakon agajin gaggawa a wurare daban daban a fadin duniya.

Yau ce ranar kungiyar bada agajin gaggawa wadda akafi sani da Red Cross a Jamhuriyar Nijar, kuma kungiyar tana taka rawar gani wajan bada taimakon gaggawa iri iri a wurare daban daban a fadin duniya.

Kungiyar kamar sauran kungiyoyi, na da ka’idoji guda bakwai wadan da take aiki da su, kuma dukkan ayyukan wannan kungiya sun ta’allaka ne a cikin wadannan ka’idojin da aka gindaya domin cimma burin kungiyar.

Alhaji Abdu Shawai shine babban jagoran wannan kungiya ta Red Cross a Jamhuriyar Nijar kuma yayi bayani dalla dalla dangane da ka’idoji da ire iren ayyukan da kungiyar ke gudanarwa. a cewar sa, babu yadda wannan kungiya zatai wani aiki ko taimakon da ya kauce ma dokokin kungiyar.

kamar yadda ya bayyana, dokokin sun hada da imani,da sa kai ba tare da wani ya tursasa maka zuwa ba, kuma aiki ne da duk na bada taimako ga duk wannda ke bukatar hakan, babu nuna son ka,i kuma duk inda aka shiga a duniya, wannan kungiya tana zaman kanta ne ba tare da taimakon wata hukuma ba domin kungiyar sa kai ce.

A cikin ire iren taimakon da wannan kungiya ta kai a Jamhuriyar Nijar kamar yadda shugaban ya bayyana sun hada da bada kudade domin gina rijiyoyin a inda ruwan sha ke karanci, abinci, wajan harkokin noma da kai daukin gaggawa musamman na magunguna da sauran makamantan su.

Ga rahoton Mani Chaibu.

Ka'idoji Bakwai Na Kungiyar Bada Agajin Gaggawa - 3'29"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG