Gwamnan yace duk ayyukan da yayi a jiharsa bai samu taimakon ko kwabo ba daga gwamnatin tarayya. Yana fatan yanzu da aka samu sabon shugaba kuma dan jam'iyyarsu komi zai daidaitu.
Gwamna Rochas Okorocha ya kara da cewa abun da ya sa a gaba yanzu shi ne maganar aiki, wato matasa da suka gama karatu amma basu samu abun yi ba. Yace zai mayarda hankali akan noma da masana'antu.
Shekaru hudu da suka gabata gwamnan yace ya gina makarantu da dama da asibitoci 27 da hanyoyi. Yace ya bada ilimi kyauta tun daga firamare har zuwa jami'a. Ko sisin kwabo ba'a biya.
Akan yadda zai jawo 'yan adawa su hada kai dashi gwamna Okorocha yace Allah ke bada mulki. Idan ya baka ba naka ba ne amma na kowa ne. Tunda an gama zabe kuma Allah ya bashi to shi na kowa ne. Yace da zara an zabeka babu batun jam'iyya kuma sai batun shugabanci. Shugabanci kuma ya hada da kowa da kowa ba jam'iyyar da mutum ya fito ba kawai. Yace yanzu duk mutanen jihar kowace jam'iyya suke suna karkashinsa.
'Yan jihar sun fadi albarkacin bakinsu. Yawancinsu sun ce gwamnan ya yi masu aiki ainun. Sun nuna farin cikinsu akan nasarar da gwamnan ya sake samu a zaben da ya gabata. Suna fatan 'yan jihar zasu bashi goyon baya domin ya kara yi masu aiki.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.