Babbar kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffukan yaki a birnin Hague, jiya Alhamis ta bada sanarwar cewa zata fara shari'ar tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, ranar 10 ga watan Nuwamban bana.
Ana tuhumar Mr Gbagbo da wani hadiminsa na kud da kud Charles Goude, da laifin cin zarafin Bil'Adama, d a suka hada da kisa da fyade, da ake zargin an aiwatar dasu bayan zaben shugaban kasar da aka yi gardama akai a 2010.
A lokacin Gbagbo yaki yayi murabus bayan da shugaban kasar na yanzu Alassane Ouattara ya kada shi, al'amari da ya janyo zanga zanga na tsawon watanni da tarzoma, kamin a kama shi Mr. Ouattara.
Ana zargin Goude shine kwamandan mayakan sakai da ake zargin da aiwtar da yawancin kashe kashen da aka yi. An kama shi ne a Ghana a 2013.