Sanata Aishatu Binani dake wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya a tarayyar Najeriya ta kafa tarihi a jihar Adamawa inda ta yi nasarar samun tikitin kujerar gwamna a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka kammala a jihar Adamawa.
Wannan nasarar da Sanata Binani ta samu dai ya sa ta zama mace ta farko da ta taba tsayawa neman takara da tikitin kujerar gwamna a jihar Adamawa a tarihin jihar.
Binani dai ta kayar da wasu maza biyar ta sami nasara karkashin inwar jam’iyyar APC kuma da wannan nasarar, Binani ta zama mace ta farko da ta lashe takarar kujerar gwamna a wata babbar jam’iyyar siyasa a jihar.
Binani sanata ce mai wakiltar Adamawa ta tsakiya ta fafata tare da doke tsohon shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Nuhu Ribadu, tsohon gwamnan jihar Adamawa Jibrilla Bindow, dan majalisar wakilai, Abdulrazak Namdas, Wafari Theman da kuma Umar Mustapha.
Da yake sanar da sakamakon zaben fidda gwanin, shugaban kwamitin zaben, Gambo Lawan, ya ce Binani ta sami kuri’u 430 inda ta kayar da abokan takararta, Nuhu Ribadu, wanda ya sami kuri’u 288 kamar yadda wakilinmu a jihar Adamawa ya ruwaito.
Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow ya sami kuri'u 103 inda ya samu matsayi na uku a jihar.
Sai dai rahotanni daga jihar Adamawa da ke yaduwa a kafaffen sada zumunta sun yi nuni da cewa baya ga rarraba wasu kayayyakin tallafi, Sanata Binani ta baiwa kowane wakilai a zaben fidda gwanin Naira miliyan 1domin a mara mata baya.
Zaben wanda aka fara da misalin karfe 11:30 na daren Alhamis an kammala shi da misalin karfe 8:44 na safiyar yau Juma’a.
Ga jadawalin adadin kuri’u da duk wanda ya tsaya neman samun tikitin gwamna a jam’iyyar APC na jihar Adamawa; Nuhu Ribadu ya sami kuri’u 288, Bindow Jibrilla ya sami kuri’u 103, Abdulrazak Namdas ya sami kuri’u 94, Aishatu Dahiru Binani ta sami kuri’u 430, Umar Mustapha ya sami kuri’u 39, Wafari Teman ya sami kuri’u 21, kuma an sami kuri'u marasa inganci 33 inda a jimlace an jefa kuri'u 923 sai jimlar aka sa rai baki daya 1009.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Lado Salisu Garba: