Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kaduna Ta Tantance Adadin Mutanen Da Aka Ceto A Makarantar Islamiya


Wadanda 'yan sanda suka ceto a wata makarantar Islamiya a Kaduna
Wadanda 'yan sanda suka ceto a wata makarantar Islamiya a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta kamala tantance adadi da kuma shekarun kananan yaran da aka ceto a wata makarantar Islamiya dake yankin Rigasa a cikin garin Kaduna, dake ikirarin koyarwar addini ga yaran da aka agajin a daddaure da mari hannud a kafa a wannan gida.

A hirar da Murayar Amurka ta yi da ita, Kwamishinan kula da harkokin mata da walwalar al’umma, da ci gaba ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Mohammad Baba, tace adadin yaran da suka samu a gidan dari da casa’in da tara ne, daga ciki kuma akwai kananan yara kasa da shekaru goma sha bakwai guda saba’in da bakwai, da kuma dari da goma sha uku da suka manyanta, wadanda daga cikin akwai dan shekaru talatin da ya ke da digiri na biyu har guda biyu a fannin lissafi, ya kuma fara karatun digirin digirgir.

Tace abinda ya fi tada masu da hankali shine ganin kananan yara ‘yan kimanin shekaru biyar da aka kai wurin wadanda daga cikinsu akwai wadanda aka ci zarafinsu aka yi luwadi dasu, daga cikinsu akwai yara goma da aka daure da mari da suka galabaita suka wahala . Banda haka ana gasa masu akuba da duka da rashin cin abinci.

Kwamishinar tace hukumomin makarantar suna hana iyaye ziyartar yaran . Ta kuma ce makarantar bata da rajista kuma babu wanda ya san da zamanta a hukumance. Ta bayyana cewa zasu nemi iyayen yaran su kuma gudanar da cikakken bincike da nufin hukumta dukan wanda aka tarar yana da hannu a kuntatawa wadannan mutane.

Wadansu iyayen da Muryar Amurka tayi hira da su sun bayyana cewa, sun biya Naira dubu tamanin da tara kafin aka karbi ‘ya’yansu a makarantar, da ake hana iyayen ziyarta sai a kalla bayan watanni uku da kai yaran.

A basu bayanan, yaran da Muryar Amurka ta zanta da su sun bayyana irin akubar da aka gasa masu a makarantar da suka hada da rataye su, da dukansu da manyan karafa da hanasu abinci, da kuma yi masu fyade. Da aka tambaye su abinda yasa basu gayawa iyayensu idan suka ziyarace su, sai suka bayyana cewa, ana kara gasa masu azaba idan ana san sun kai kara.

Daga cikin wadanda aka ceto akwai wadanda suka shafe shekara goma a gidan, da suka fito daga ciki da wajen Najeriya.

A nasu bayanin, malaman allo sun bayyana cewa basu san da zaman wannan makaranta ba da suka ce makarantar Islamiya ce ba ta allo ba. Suka kuma yi allahwadai da wannan lamarin da suka bayyana a matsayin keta hakin bil’adama da cin mutumci.

Tuni jami’an tsaro suka kama mutane bakwai da ake zargi da tsarewa da kuma cin zarafin mutanen da suka hada da shugaban makarantar mai suna Isma’il Abubakar da bayan kamala bincike za a gurfanar dasu gaban kotu.

Saurari cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Isa Lawal Ikara ya hada mana

An tantance adadin yaran da aka ceto a makarantar islamiya-6:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG