Gwamnatin mulkin sojan Junhuriyar Nijar ta ce za ta inganta matakan tsaro don kare ma’aikatan agaji na kasa da kasa, bayan da aka sami rahoton barazana ga lafiyar ma’aikatan daga kungiyoyin da ke da alaka da al-Qa’ida. Jami’an aikin agaji sun ce barazanar za ta gurgunta kokarinsu na ciyar da mutane miliyan 8 da ke fama da yunwa a kasar ta Yammacin Afirka.
Da alamar dai barazanar ta fi karfi ne a yankin Maradi na kasar ta Nijar, da ke gabashin babban birnin kasar, Niamey, da nisan kilomita 600. Gwamnan Maradi, Kanar Garba Maikano, ya ce babu wani takamaiman bayani game da barazanar. To amman ya ce gwamnati na kokarin tantance kasashen dukkannin wadanda ba ‘yan Nijar ba da ke wannan yankin don ta samar da ingantattun matakan tsaro ga muhallinsu.