Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutane Dubu 200 Da Matsugunansu A Jamhuriyar Nijar


Wani hoto na kungiyar Oxfam da aka dauka ranar 17 Augusta 2010 ya nuna mutane tsaye a kusa da wasu gidajen da ruwan ambaliya ya rushe a birnin Zinder.
Wani hoto na kungiyar Oxfam da aka dauka ranar 17 Augusta 2010 ya nuna mutane tsaye a kusa da wasu gidajen da ruwan ambaliya ya rushe a birnin Zinder.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi rokon da a tallafawa Nijar cikin gaggawa saboda ambaliyar da ta biyo bayan mummunan karancin abincin da ake fama da shi a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi rokon da a tallafawa Jamhuriyar Nijar, inda ta ce ambaliyar ruwa a cikin 'yan makonnin nan ta raba mutane kusan dubu 200 da gidajensu.

Ofishin kula da Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya yace ana da bukatar gaggawa ta kayayyakin gina muhalli da barguna. Haka kuma, ana karancin abinci da gidajen sauro.

Wannan ambaliya tana kara munin halin jinkai da ake fama da shi a Jamhuriyar Nijar, kasar da tun farko ta ke fuskantar mummunan fari da kuma karancin abinci kafin wannan ruwan sama da ya taho kamar da bakin kwarya.

Ruwan ambaliyar ya wanke shuke-shuke kalilan da suka fara tsirowa a kasar.

Wata wakiliyar kungiyar agajin kasar Britaniya mai suna Oxfam a Nijar, Caroline Gluck, ta fadawa Muryar Amurka a makon jiya cewa mutane sun shiga cikin wani mummunan hali na kaka-ni-ka-yi.

XS
SM
MD
LG