Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Farko Sam Ba Mu Dauki Maganar IPOP Da Muhimmanci Ba –  Rochas Okorocha


'Yan Kungiyar Fafukar Kafa Kasar Biafra IPOB
'Yan Kungiyar Fafukar Kafa Kasar Biafra IPOB

Tsohon gwamnar Jihar Imo Rochas Okorocha ya ce sam basu dauki fafatukar da tsagerun kungiyar IPOB ke yi da wani muhimmaci ba, kuma basu dauka za ta girma har ta zama damuwa ga Najeriya ba.

A yayin da yake zantawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Rochas Okorocha, wanda yanzu haka dan majalisar dattawan najeriya ne, ya ce tun kafin ya hau kujerar Gwamnan Jihar Imo, mutanen yankin su ke yi wa batun tsagerun kungiyar ta IPOB mai hankoron kafa kasar Biyafara rigon sakainar kashi.

Rochas Okorocha
Rochas Okorocha

Rochas na mai da martani ne akan zargin shugabannin kabilar Ibo da yin shiru akan ayukan 'yan kungiyar ta IPOP, da ke barazana ga tsaro, da suka hada da kai hare-hare akan hukumomi da jami'an gwamnati, da kuma kai hari ga 'yan Arewa mazauna yankin.

‘’Da farko Mun dauki maganar kungiyar IPOB da wasa, mu na ganin ta kamar wasan yara, yaran da ba su da aikin yi wadanda ke son a san da zaman su, amma abin mamaki ne yadda ta girma har ta zama matsala ga Najeriya ga baki daya’’ in ji Sanata Okorocha.

Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra,
Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra,

Haka kuma ya kara da cewa a lokacin da yake Gwamna, ya ba da shawarar bin lamuran kungiyar a hankali ba tare da an hada da karfin soji ba amma ba’a dauki shawarsa ba.

"Na taba samun labari lokacin ina Gwmana cewar yaran su na son su yi tawaye a IMO, sai na kira wani taro da dukkan hukumomin tsaro a jihar na ba da umarnin kar mu yi amfani da karfi domin zai iya sa yaran su kara kangarewa."

Ya ci gaba da cewa "hakan kuwa aka yi, yaran suka shigo jihar suka yi ta wasansu har suka gaji, na fito na gansu a gindin bishiya suna shan ruwan leda duk sun gaji, sai na yi godiya ga Allah."

Ya ce da an bi shawararsa da farko wajen bin yaran a hankali da lamarin bai kai yanda yake ba a yanzu ‘’domin idan yaran suka gaji za su fara fada a tsakaninsu, su kuma sake raba kansu."

Tsohon gwamnan ya ce rashin yi wa mabiya bayani na gaskiya akan al'amura ne ke kara sa matasan yankin a cikin yanayin.

To sai dai Okorocha ya jaddada cewa rashin aikin yi a tsakanin matasan na daya daga cikin abubuwan da suka kara hura wutar wannan lamari, ta yadda ake samun sauki wajen saka matasa a ayukan ta'addanci.

Akan haka ya ba da shawarar da a gudanar da Gwanati ta al’umma wacce za ta hada Sarakuna da shugabanin alumma wadanda za su zauna da yaran su ji damuwarsu.

"Yaranmu ne na cikin gida wadanda ba su da wani kwakwarar sana’a da za su taimaki iyalansu, su ne yan Kungiyar IPOB, kuma idan ka tambaye su minene IPOB ba su sani ba, sai dai su ce maka ba’a son mu don mu kabilar Ibo ne, Fulani sun ki mu , Hausawa ma ba sa son mu’’.

Don haka Okorocha ya yi kira ga gwamnati da ta rungumi tattaunawa da shugabannin yankin musamman sarakunan gargajiya, wadanda kuma suna da kima da daraja ga matasan, ta yadda za'a sami warware wannan matsala cikin sauki.

Saurari hira da Rochas Okorocha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG