Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jones Na Jam'iyyar Democrat Ya Lashe Zaben Alabama


Doug Jones
Doug Jones

Doug Jones ‘dan jam’iyyar Democrat ne ya lashe zaben da aka gudanar na musamman don cike gurbin kujerar Majalisar Dattijai a jihar Alabama dake kudancin Amurka.

Bayan yin kamfen mai cike da rikici, masu kada kuri’a sun zabi Jones maimakon Roy Moore ‘dan jam’iyyar Republican.

Wannan nasara da ya samu na nufin cikin wajen Janairu bayan an rantsar da shi, ‘yan jam’iyyar Republican dake da rinjaye a Majalisa zasu ragu su koma 51 da 49, kuma hakan ya karawa shugaba Trump wahala wajen gudanar da ajandarsa.

Jones ya zamanto ‘dan Jam’iyyar Democrat na farko daya sami lashe kujerar ‘dan Majalisar Dattijai daga Alabama tun shekarar 1992.

Moore dai ya sami goyon bayan shugaba Trump, amma ya fuskanci adawa daga sauran shugabannin jam’iyyarsa. An zarge shi da yin lalata a shekarar 1970 lokacin da matan da suke zarginsa suna matasa, shi kuma yana ‘dan shekaru 30.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG