Jaridar da ake wallafawa a shafin internet ta Aviation Herlad da ke buga bayanai akan harkokin sufurin jirage, ta wallafa cewa, an samu sakon ne daga cikin ban daki, gab da jirgin zai fada cikin tekun.
Jaridar ta ce ta samu wadannan bayanai ne ta kafar fasahar nan da ke bin diddigin bayanan jiragen sama, inda na’urar ta nuna cewa an samu tashin hayaki a ban daki da misalign karfe 2.26 na safiyar agogon yankin.
Bayan haka kuma, an kuma jsamu wani sakon gaggawa misalin minti guda bayan sakon farkon, sannan daga baya na’urar ta nuna alamun tashin hayaki ko kuma wuta a kusa da kayayyakin wuta da ke cikin jirgin.
Tuni dai hukumar da ke kare aukuwar hadurran jirage ta kasar Faransa ta tabbabatar da aukuwar wannan lamari, sai dai wani kakakin hukumar ya ce ya yi wuri a ce ga takamaiman abinda ya hadadsa hadari idan har ba samu sauran takarkacen jirgin ba ko kuma akwatin nadar bayanai na Black Box.
A daya bangaren kuma, yanzu haka an kara tsaurara matakan tsaro a duk filayen tashin jiragen sama da ke fadin nahiyar turai, yayin da ake cigaba da laluben abin da ya haddasa hadarin jirgin na kasar Masar.
A can filin tashin jirage na Paris inda jirgin na Masar ya dauko tafiyarsa, ana waiwaye kan irin tsarin tsaron da ke filin jirgin, tare da gudanar da bincike kan ma’aikata sama da dubu 90 da ake aiki a wurin, ciki har da masu kula da kayayyakin fasinja.
Wasu kwararru a fannin tsaron nahiyar turai sun ce idan dai har wani abin fashewa aka dasa a cikin jirgin, to akwai yuwuwar an dasa shi ne a arewacin Afrika ko kuma kasashen da ke gabashin Afrika inda jirgin ya yada zango kafin ya doshi birnin Alkahira.