Gwamnatin jihar Taraba ta musanta rahotannin dake cewa an samu bullar cutar COVID-19 a jihar, ta kuma sassauta dokar hana zirga-zirga don ba jama’a damar zuwa kasuwanni.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Dakta Innocent Vakai, ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma kiyaye gargadin da likitoci ke yi na yadda za a kauce wa kamuwa da cutar.
A jihar Adamawa kuma ana ci gaba da ce-ce-ku-ce game da tallafin da gwamnatin jihar ta bada ga masu sana’ar kabu-kabu wato 'yan Keke-NAPEP na naira miliyan 20, da kuma kayyakin da aka ba kananan hukumomi.
Yayin da wasu ke murnar samun tallafin, masu larura ta musamman wato nakasassu sun koka, sun ce har yanzu basu ga nasu rabon ba.
Masanin harkar shari'a Barista Sunday Joshua Wugira, hadimin gwamnan jihar a fannin harkokin al’umma, ya ce gwamnatin jihar na daukar matakan ganin an taimaka wa nakasassu.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum