Kawo yanzu dai adadin masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya mutum 276 ne a cewar cibiyar dakile cututtuka a Najeriya NCDC.
Baya ga haka an sallami masu jinya 44, kuma mutum 6 sun rasa rayukansu.
Yanzu haka ma likitocin kasar China sun sauka Najeriya domin taimakawa wajen yaki da wannan cutar.
Jihar Legas ita ce ta daya wajen yawan masu dauke da wannan cutar inda take da mutum 145, yayin da binin tarayya Abuja ke da 54.
A sanarwar da cibiyar ta fitar, ta ce an samu karin mutum 22 masu dauke da cutar a Najeriya.
Cikin mutane shidan da suka rasu har da wani dan kasar Birtaniya wanda ya shigo kasar daga Indiya, kana ya ratsa Legas.
Hukumomi dai sun ce ya shigo da cutar ne Najeriya.
A waje daya kuma, jami’an lafiya daga kasar China su 15 sun sauka a Najeriya tare da kayan aiki da magunguna domin bada gudunmawaru ta
kawo karshen wannan cuta da ta samo asali daga kasar ta Chinar.
Wani babban kamfanin injiniyoyin kasar China ita ce ta hada kai da gwamnatin Najeriyan domin bada gudunmawar kawo karshen cutar cikin gaggawa.
Facebook Forum