Wani harin jirgi mara matuki da Amurka ta kai ya auna Shugaban Taliban a Pakistan a wani lardi a Afghanistan,wanda ke daura da kan iyakar Pakistan, abin da wani jami'in sojin Amurka ya tabbatar ma Muryar Amurka kenan. Wani rahoton da ya fito daga mazauna wurin, wanda ba a tabbatar ba, ya nuna cewa an hallaka Mullah Fazlullah.
Jami'in na sojin Amurka, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce harin, wanda aka kai da tsakar daren ranar Laraba, an auna shi ne kan Fazlullah, Shugaban Tehrik-e-Taliban, shiyyar Pakistan.
Zuwa yanzu dai jami'an Hedekwatar Tsaron Amurka sun ki cewa komai kan ko shin an yi nasara a harin ko a'a.
Jami'an na sojin Amurka sun ce Fazlullah ya bayar da umurnin kai wasu muggan hare-hare da dama kan muradun Amurka da Pakistan tun bayan da aka nada shi jagoran kungiyar a 2013, ciki har da hari kan makarantar soji ta Peshewar da ya yi sanadin mutuwar mutane 151, ciki har da yara sama da 130.
Facebook Forum