Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Bayelsa Za Ta Fara Koyar Da Harsunan Ijaw, Faransanci, Da Sinanci A Makarantu


Wasu dalibai
Wasu dalibai

Gwamnatin Bayelsa ta ce za ta ba da fifiko kan koyo da koyar da harsunan Ijaw, da Faransanci, da kuma Sinanci a makarantun gwamnati a jihar.

WASHINGTON, D. C. - Mataimakin gwamnan jihar, Mr. Lawrence Ewhrudjakpo ya bayyana a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Doubara Atasi, ya fitar a jiya Alhamis cewa, karuwar tasirin tattalin arzikin kasar China a harkokin duniya a matsayinta na babbar jigo a harkokin cinikayya da cinikayyar duniya, ya nuna kamatar tabbatar da shigar da karshen kasar China a cikin manhajar karatu.

Ewhrudjakpo ya bayyana cewa, gwamnati zata fi maida hankali kan harsunan ne domin, baya ga muhimman darussa na kimiyya, harsunan zasu taimaka wajen samar da yaran da za su ci gajiyar damar sana’ar da wadannan darussa ke bayarwa a nan gaba.

Ana magana da harshen Ijaw ne a yankin Niger Delta da ya kunshi jihohin Delta, Bayelsa da kuma Cross Rivers. Akwai kuma wadannan suke harshen da ake kira “Arogbo-Ijaw” a jihar Ondo.

A shekarun nan, masana na jadada bukatar ganin gwamnatoci sun dauki matakan raya al’adu da harsuna da ake gani aka kara watsi da su sabili da ci gaba na zamani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG