Tsohon shugaban kasar Ghana ya rasu da sanyi safiyar ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba.
Wakilin Muryar Amurka a Ghana ya tabbatar da rasuwarsa a asibitin koyarwa na Korle Bu da ke Accra, inda aka kwantar da shi.
An haifi John Rawlings a ranar 22 ga watan Yuni 1947, kuma shine shugaban kasa na farko a jamhuriya ta 4, da ya jagoranci kasar daga watan Janairun 1993 zuwa Janairun 2001, wanda ya yi wa’adin mulki biyu da doka ta iyakance.
Kafin nan, shi ne shugaban mulkin soja daga Disambar 1981 zuwa Disambar 1992, da ya hau karagar mulkin a wani juyin mulkin soja.
Rawlings tsohon sojan sama ne da ya fara shiga faen siyasar Ghana a ranar 15 ga watan Mayu 1979 a lokacin da ya jagoranci wani rukunin sojojin saman Ghana na wani juyin mulki da baiyi nasara ba da hakana yasa aka kama shi aka kai shi gidan yari.
An kuma yi masa shari’a kotun sojoji a bayyanar jama’a kuma aka yanke masa hukunci kisa. Saboda yadda ya nuna kishin kasa a jawabansa da yake kare kansa, an san shi a ko’ina a cikin kasar a matsayin dan kasar Ghana na hakika, kuma ana masa lakabi da Juniro Jusus, asalin inda ya samo “JJ”.
Tun dai 'yan kasar ta Ghana suka fara mika sakon ta'aziyyar su ga iyalansa da kuma gwamnatin kasar.
Facebook Forum