Da yake jawabi a wani taron 'yan jarida a birnin Accra, ministan watsa labaran kasar ta Ghana Kojo Oppong Nkrumah, ya ce kasar ta sake shiga hatsarin yiwuwar barkewar annobar sakamakon bude filayen jiragen saman ta domin zirga-zirgar kasa-da-kasa.
To sai dai ya ce gwamnatin kasar ta lura da yadda cutar ta ke waiwayen baya a wasu kasashen duniya, musamman a nahiyar Turai, Asia da kuma Amurka, bayan da suka yi nasarar shawo kan annobar da farko.
A cewar ministan, ya zama wajibi gwamnati ta sake daukar matakai cikin lokaci, domin ganin cutar ba ta sake dawowa ba a kasar ta Ghana, domin kuwa masana kimiyya sun yi gargadin cewa zagaye na biyu na annobar, shi ne mafi muni da tsanani da kuma ban tsoro.
Akan haka Nkrumah ya ce za'a kara tsaurara matakai a filayen jiragen sama, tare da sanya ido da kuma yin gwaji akan dukkan fasinjojin da ke shigowa, makwanni biyu bayan da aka bude filayen jiragen kasar.
Sai dai wata kwararriya a fannin kiwon lafiya a kasar Dr. Maryam, tana ganin kamata ya yi gwamnati ta kara maida hankali sosai akan yaduwar cutar na cikin gida, a maimakon masu shigowa kasar daga wasu kasashe.
Ta ce "tun kafin a rufe filayen jiragen sama, alkaluma sun bayyana cewa yawan yaduwar cutar na cikin gida a tsakanin mutanen da ba su je ko ina ba, ya zarta na masu shigowa da cutar."
Ta kuma ba da shawarar kara maida hankali akan matakan saka takunkumin rufe baki da hanci, yawan wanke hannu da sinadarin kashe kwayoyin cuta, ba da tazara a tsakanin jama'a da kuma kaucewa tarukan jama'a.
Ga cikakken rahoton Ridwan Abbas:
Facebook Forum