Rahotannin daga garin Tilaberi na Janhuriyar Nijar na cewa, a jiya juma’a da daddare da misalin karfe 9 wasu mutane kimanin 5, a cikin wata farar mota dauke da bindigogi sun kai hari a wani shingen duba ababen hawa na ‘yan sanda a kauyen Tilakaina da ke dab da fita daga Tilaberi kan hanyar zuwa Ayorou.
Bayan musayar wuta ta wani dan lokaci ‘yan sandan sun yi nasarar murkushe wannan harin, wanda yayi sanadiyar mutuwar dan bindiga mutum daya.
Sannan daga bangaren ‘yan sanda an samu rauni, yayin da sauran maharan suka juya inda suka fito.
Wata majiya mai zaman kanta ta ce, an yi wannan nasara ne da jajircewar wata ‘yar sanda da ta labe a ofishin nasu lokacin da takwarorinta maza suka gudu. Amma har yanzu gwamnatin ba ta ce komai ba game da harin ba.
Yankin Tilaberi mai makwabtaka da kasashen Mali da Burkina Faso, ya na cikin yankunan da ke karkashin dokar ta baci a Jamhuriyar Nijar sakamakon yawaitar kai hare-hare na ta’addanci a yankin.
Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma:
Facebook Forum