Yau ne Janaral Buhari zai kaddamar da kemfen dinsa a birnin Yola fadar gwamnatin Adamawa.
Rundunar 'yansandan jihar ta ja kunnuwan jama'a game da keta hotunan 'yan takara da kuma tada hargitsi. Kwamishanan 'yansandan jihar Mr. Gabriel yace zasu saka kafa cikin wando daya da 'yan siyasan dake barin magoya bayansu suna yiwa abokan hamayyarsu barna.
Yace duk wanda aka ga yana keta hotunan wasu 'yan takara rundunar zata cafke shugabanninsu. Yace babu sassauci ga kowa komi matsayinsa.
Wasu 'yan jam'iyyun siyasa sun ce abun da kwamishanan ya fada dahir ne. Bai kamata ma 'yan siyasa su jira kwamishanan ya ja masu kunne ba. Su da kansu ya kamata su su kwabi magoya bayansu idan har ana son zaman lafiya a jihar..
Ya zama wajibi a yi zaben cikin zaman lafiya domin 'yan takaran dake neman zabe duk suna yi ne domin al'ummarsu kuma dukansu abokan juna ne kowace jam'iyya mutum yake. Akwai wadanda 'yan gida daya ne amma suna jam'iyyu daban daban. Zabe ba yaki ba ne ko wani zarafi na nuna kiyayya.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.