Akwai kuma kararraki fiye da dubu daya a gaban kotu kuma an yi nasarar dawo da nera fiye da miliyan dubu dari uku cikin aljihun gwamnati.
Mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo shi ya tabbatar da hakan a zauren muhawara na mataimakan 'yan takaran shugaban kasa na zaben ranar 14 ga wannan watan.
To saidai mataimakin dan takarar jam'iyyar APC Farfasa Osinbajo ya ki amsa gayyatar zuwa zauren muhawarar. Akan batun cin hanci da rashawa kuwa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar UDP Haruna Adamu yace idan aka zabesu zasu gwada misali akan mutum daya ko biyu shi ke nan cin hanci zai zama tarihi a Najeriya.
Akan matsalar tsaro mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo yace ta shafi kasashen duniya da dama ba Najeriya kadai ba. Amma gwamnati zata kara dagewa wajen samar da kayan aiki da horas da sojoji domin a samu nasara kan yakin. Yace ko a ranar daya ga wata an kwato kananan hukumomin Adamawa da dama daga kungiyar Boko Haram.
To saidai mataimakin dan takarar shugaban kasa na UPP Bello Umar yace matukar aka baiwa sojoji dama zasu iya yaka rBoko Haram cikin mako biyu har ma da Afirka gaba daya.
Jam'iyyar APC da taki halartar muhawarar ta zargi wadanda suka shirya taron a matsayin 'yan amshin shatan gwamnati ne da suka hada da gidan telebijan na kasa, NTA da Radiyon Najeriya.
Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.