Lakcan ya mayarda hankali ne akan haduran dake tafe da shiga yamutsi musamman a lokutan zabe.
Kungiyoyin matasa da na mata da kuma cibiyoyin radun cigaban al'umma suka halarci taron wanda kungiyar matasan Najeriya da hadin gwiwar kungiyar kiristocin Najeriya suka shirya a cibiyar bincike da bada horo kan harkokin dimokradiya ta Mambayya a Kano.
Musa Usman shi ne ya rabtaba hannu akan yarjejeniyar a madadin kiristocin Najeriya reshen Kano. Yace burinsu wannan karon shi ne a yi zabe mai lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana. Yace sun cimma yarjejeniya kuma sun kaiga matsaya. Kowa ya yadda kana akwai takardun da suka sanyawa hannu. Yace zasu gudanar da kansu cikin yanayi mai kyau kafin a yi zabe da lokacin zabe da kuma bayansa. Basu yadda wani dan siyasa ya baiwa matshi kudi ba ya je ya sha wani abu da zai harzukashi ya tada hankali ba.
Ibrahim Wayam wanda ya sanya hannu a madadin matasan muslman Kano yayi karin haske. Yace sun yadda kiristoci zasu idar da sakonsu a mijami'u kana musulmai zasu kai nasu masallatai da nufin duk al'umma su sani su kuma himmatu. Akwai wani kwamiti da za'a kafa bayan taron Kaduna wanda zai hada da shugabannin jam'iyyun siyasa domin fadakar dasu. Kokakri ne na dakile duk wani kokarin da 'yan siyasa zasu yi domin yin anfani da matasa domin tada hankali da tarzoma. Musulman da kiristocin sun yadda su zama 'yanuwan juna iyakar ransu.
Ga cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari