A yau lahadi ‘Yan sandan Jamus sun bayyana cafke shugaban yankin Catalonia da aka tunbike, Carles Puigdemont, yayin da yake kokarin tsallaka kan iyaka kasar ta Jamus zuwa kasar Denmark.
A shafinsa na Twitter, Lauyan Puigdemont, Alonso- Cuevillas, ya tabbatar da kama tsohon shugaban yankin na Cataloni.
Ya kara da cewa, Puigdemont na kan hanyarsa ce ta zuwa Belgium, a lokacin da aka fitar da takardar iznin kama shi.
Hukumomin Spaniya ko kuma Andalus na neman Puidgemont ne saboda rawar da ake zargin ya taka a zaben raba-gardamar da aka yi na ballewar yankin na Catalonia a bara.
Wannan kamu da aka yi wa Puigdemont, na zuwa ne bayan da wata kotun kolin Spaniyan ta yanke shawarar a tuhumi shugabannin yankin na Catalonia da laifuka 13, kan bore da suka nuna da wasu laifuka da suka jibinci yunkurin ballewa daga kasar.
‘Yan sandan na Jamus, sun yi nasarar kama shugaban yankin na Catalonia ne ta hanyar amfani da takardar iznin kama mutum ta kasa-da-kasa, wacce kasar ta Spaniya ta samar.
Idan har aka same shi da laifi, Puigdemont zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekaru 25.
Facebook Forum