'Yan jam'iyyar PDP da 'yansandan jihar Jigawa suka kama sun je garin Bamaina ne domin ganawa da Sule Lamido tsohon gwamnan jihar, kuma jigo a jam'iyyar.
Amma acewar ASP Abdul Jinjiri kakakin rundunar 'yansandan jhar yace sun dauki matakin maka mutanen ne biyo bayan samun rahotannin siri dake cewa suna dauke da makamai.
Jinjiri yace lallai sun kama mutanen da makamai kuma makaman suna hannunsu da matasan da suka kama su dari da arba'in da takwas. Kawo yanzu ma tuni aka tasa keyarsu zuwa kotu.
Biyo bayan kama matasan Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin shi Alhaji Sule Lamido akan lamarin. Yace wajen wata shida baya duk sati akalla mutane cikin motoci hamsin ko fiye zasu zo wurinsa. Yace za'a hana zumunci ne. Injishi kodayaushe yana zuwa ta'aziya da bikin daurin aure. Yace idan mutane sun taso daga Sokoto ko Enugu cikin motoci hamsin ko fiye sai ya gayawa 'yansanda su bashi izini domin za'a zo a gaisheshi?
Ya kira masu mulki su yi mulki masu hamayya kuma a barsu su cigaba da hamayya. Wannan ita ce siyasa.
Ga rahoton Mahamud Ibrahim Kwari da karin bayani.