Sule Lamido tsohon gwamnan jihar Jigawa yace tunda an ce basu da lafiya bai kamata a damu dasu ba.
Amma shi ya san suna nan da rai kuma kwana kwanan nan aka yi bikin karbar wasu dubu ukku a jihar Jigawa duk da cewa bangarorin biyu na jam'iyyar na cigaba da ja da juna. Yace duk da rashin lafiyar jam'iyyar tana motsi a jihohi da dama tare da cin zabe.
Lamido, acewarsa hukumar zabe ko INEC da 'yansanda da kotu babu ruwansu da jam'iyyar PDP. Idan su da suke shugabanni basu da sanin hakkin shugabanci babu wanda zai gyara masu. Dole ne su yi gyara da kansu ba kotu ba ko 'yansanda.
'Yan PDP ya kamata su san cewa akawai hakki na shugabanci a kansu. Yace sun yi mulki na shekaru goma sha shida an zo an yi karya an yi damfara an kawar dasu daga mulki. APC din ta hau mulki a Najeriya amma ta kasa yin komi. Injishi yanzu jama'a suna cewa sun yi kuskure a yi masu ahuwa. Saboda haka ya kira 'yan jam'iyyar da su warware rikicinsu domin a samu sahida.
Garahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.