Masu zanga-zangar adawa kenan suke rera waka jiya Litinin a gaba jami’ar Yaounde a babban birnin kasar Kamaru.
Abin da wakar ke cewa shine shugaban ‘yan adawa Maurice Kamto shine ya lashe zaben shugban kasa na ranar 7 ga watan Oktoba, kuma kamata yayi dadadden shugaban kasa Paul Biya ya mika masa mulki.
Yawan jami’an ‘yan sandan da aka aika shine ya sa masu zanga-zangar suka dakatar da yin wakarsu a cikin jami’ar.
Jami’ai dai sunce Biya ya lashe zaben ne da kashe 71 cikin 100 na kuri’un da aka kada. Mai biye masa shine Kamto wanda ya samu kashe 14 na kuri’un.
Jam’iyyun adawa dai sun zargi jam’iyya mai mulki da tafka magudi a zaben.
Facebook Forum